
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leverkusen ta kori Erik Ten Hag, wanda tsohon kocin Manchester United ne bayan buga wasanni uku ba tare da samun nasara a ko ɗaya ba.
Leverkusen ta samu maki ɗaya ne kacal bayan wasanni biyu da ta buga a Bundesliga.
Ƙungiyar ta ɗauki Erik Ten Hag a matsayin kocinta ne bayan da Manchester United ta raba gari da shi a watan Oktoban shekarar da ta gabata.
A sabuwar yau ƙungiyar ta aika masa da saƙon sallama daga horar da ƴan wasan nata, kamar yadda ɗan jarida Fabrizio Romano ya ruwaito.
