
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya saɗaɗa ya goge wani rubutu da ya wallafa a Soshiyal Mediya bayan da al’umma suka riƙa sunansa kan rubuta kalmar ‘brillion’ a madadin ‘billion’, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A yau Litinin al’amarin ya faru a lokacin da Shugaba Tinubu ya yi wani rubutu da ke bayyana ayyukan da gwamnansa ta yi a shafinta na X.
Ga yadda rubutun yake kamar yadda jaridar IntelRegion ta ɗauko:
“I took
an oath to serve all Nigerians, not a section. That oath guides every bridge, road, rail, power, and health project we deliver.
“From the Lagos–Calabar Highway in the South to the Sokoto–Badagry Superhighway in the North; from Port Harcourt–Maiduguri rail in the East to Abuja–Kaduna–Kano expressway in the Centre, and the Trans-Saharan highway connecting African countries, these are not local trophies. They are our national assets.
“Health centres are being rehabilitated nationwide, light rail projects in Kano, Kaduna, Lagos & Ogun have been given the green light, 250,000 jobs are being created, power is returning to Kaduna through the revived 255MW power plant, bridges in Onitsha & Bonny reconnect our people, oil exploration is expanding in Bauchi & Gombe, and the AKK pipeline has crossed the Niger.
“Every farmer who needs a road, every trader who needs power, every child who needs a school, every patient who needs care… this is who we are building for.”
“This is the equity of Renewed Hope. No Nigerian is second class, no region is left behind. Together we will rise as one nation, one people, and one destiny.”
Saidai, duk da cewa an goge rubutun, an gano cewa hatta hotunan da rubutun ke ɗauke da su akwai kurakurai wajen rubutu wasu kalmomi irinsu ‘countiries’ a madadin ‘countries’ da ‘brillion’ madadin ‘billion’ da wasu da suka shafi musanya shiyyoyin sassan Nijeriya.
Jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyinsu akan haka, inda wasu ke ganinsa a matsayin wani ɓangare na taɓarɓarewar al’amuran gwamnatin.
