‘Yan sanda a Katsina sun kama mutane biyu masu safarar makamai

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mutanen da suka fito daga Hadejia kan hanyar su ta zuwa Safana sun shiga hannu ƴan sanda ne a hanyar Ingawa zuwa karkarku.

Bayanin haka ya fito da ga kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro a Jihar Katsina Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa a wata takardar sanarwa da ya fitar.

Ya ce ƴan sanda sun kama mutanen ne a cikin wata mota ƙirar Volkwagon Golf mai numba RSH528 ɗauke da miyagun bindiga mai sun General purpose machine Gun(GPMU) tare da harsashi 1,063 na AK47 da wasu harsashi guda 232 PKT.

Waɗannan mutane Abdulsalam Muhammad ɗan shekara 25 da Aminu Mamman ɗan shekara 23 sun fito daga Hadejia kan hanyar su ta zuwa Safana.

Dr Danmusa ya sanar da cewa ƴan sanda sun fara binciken inda zasu kai wannan makamai da gano ko akwai wasu mutane da suke aikata wannan ta’addanci da kuma daga ina ne makaman suka fito.

Ya ce da zaran yan sanda sun gama gudanar da bincike za a gurfanar da su a kotu.

By ukarofi