Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rumbun sauƙi shiri ne da gwamnatin Katsina ta ɓullo da shi na sayar wa ma’aikatan jihar da kayan masarufi a bisa farashi mai sauƙi.
Gwamnatin Katsina za ta saidawa ma’aikatan kayan abinci da suka haɗa da Shinkafa da taliya a farashi na rabin abinda gwamnati ta saya wanda a ƙarshen wata za a cire kuɗin daga albashin ma’aikatan.
Akwai shagunan Rumbun Sauki a kowace ƙaramar hukumar 34 da ke jihar,kuma ana sa ran gwamnati za ta buɗe shagunan a rumfunan zaɓe guda 361 da ke jihar.
A hira da manema labarai shugaban ƙungiyar ƙwadago kwamred Hussaini Hamisu Yanduna ya yabawa gwamnatin Dikko Raɗɗa da ta fito da wannan tsari ga ma’aikatan jihar.
Ya ce babu shakka wannan shiri ya taimakawa ma’aikatan jihar wajen rage halin ƙuncin rayuwa da alummar ƙasa suka shiga musamman ma’aikatan gwamnati.
Kwamred Yanduna sai yayi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta faɗaɗa wannan shiri ta hanyar samar da ƙarin kayan masarufi da ma’aikata za su sami natsuwa.
“Ina kira ga gwamnatin malam Dikko Raɗɗa da ta sanya Masara,Gero, Dawo,mai na girki,su mafi da sauran cikin shirin Rumbun Sauƙi wanda haka zai taimakawa ma’aikata su sami sauƙin rayuwa.
Shugaban ƙungiyar ya bayyana wasu nasarori da ya samu daga lokacin ya hau kujerar shugaban ƙungiyar.
“A lokaci na ne gwamnatin tarayya ta kara albashi mai ƙarancin na Naira dubu 30 daga baya ta naira dubu 70 wanda a nan jihar Katsina ba a ɗauki tsawon lokaci ba aka fara biyan sabon tsarin albashi,”inji kwamred Yanduna.
Haka kuma ma’aikacin ƙaramar hukumar a jihar yana iya kaiwa matakin albashi na 16 har zuwa lokacin da zai ajiye aiki ba kaman a da iyakar ma’aikacin ƙaramar hukuma ya kai matakin albashi na 15, wannan ma nasara ce a gare shi ya ce.
Kwamred Hussaini Yanduna ya bayyana gina sakatariyar ƙungiyar na NLC reshen jihar a matsayin shima nasara a gare sa .
Sai dai shugaban yayi kira ga gwamna Dikko Raɗɗa da ya bincika yadda ma’aikata ke samun matsala na rashin kulawa a asibitocin da sukayi rajista ƙarƙashin shirin taimakekeniya na kiwon lafiya.
