An kai wa ayarin Malami farmaki a Birnin Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Da yammamacin ranar Litinin ɗin nan ne waɗansu mutane ɗauke da sanduna da adda suka farmaki ayarin tsohon ministan shari’a Alhaji Abubakar Chika Malami a cikin garin Birnin Kebbi a lokacin da ya ke kan hanyar zuwa gidan sa bayan dawowar sa daga garin Yauri wajen gaisuwar rasuwa.
Malam Muhammed Nasir wanda a gaban sa abin ya faru ya shaida wa wakilin Blueprint Manhaja da cewa waɗansu gungun matasa ne da ake sa ran magoya bayan gwamnan Jihar Kebbi ne Malam Nasir Idris suka tare hanya suka rinka jifar ayarin motocin da Abubakar Chika Malami ya ke tare da magoya bayan sa.
Ya ƙara da cewa an raunata mutane da dama kuma an farfasa gilashi tare da buge motoci da dama har sai da ‘yan sanda suka fara harbi sannan mutanen suka gudu.

By ukarofi