Yadda ƴan dabar siyasa suka farmake ni a Kebbi – Malami

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi zargin wasu ƴan dabar siyasa sun farmaki tawagar motocinsa a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.

A wata sanarwa da ya fitar yau Talata, Malamin ya bayyana al’amarin a matsayin abin takaici a tarihin siyasar jihar, inda ya zargi wasu manyan mutane a jihar da ɗaukar nauyin harin.

Ya ce, al’amarin ya auku ne a ranar Litinin a lokacin da ya ke dawowa daga ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Gwandu da iyalan marigayi Imam Tukur Kola.

A cewarsa, lamarin ya faru ne gidansa da ke kusa da hedikwatar jam’iyyar APC.

“An jefe mu da duwatsu da abubuwa masu haɗari, motoci sun lalace, sannan mutane da dama sun samu raunuka har da kujewa”, inji Malami.

Ya yi zargin farmakin abu ne da ke da alaƙa da siyasa, yana mai cewa ƴan gaba dai-gaba dai na jam’iyyar da makusantan gwamnan suna wajen da abin ya faru.

Haka kuma ya zargi jami’an tsaro da goyon bayan abinda aka masa kasancewar wasu daga cikin maharan sun tsere zuwa cikin hedikwatar ba tare da an kama su ba.

By Babaji