NYSC ta biya ƴan hidimar ƙasa alawus na hutun wata biyu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da ɗalibai masu yi wa ƙasa hidima NYSC, fara biyan ƴan hidimar ƙasa kuɗaɗen da suke bi bashi a ranar Laraba. Lamarin da ya zama na farko tun ranar 3 ga Yuni da aka tafi hutun wata biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa biyan su kuɗaɗen yana da alaƙa da sabon alawus na N77,000 da Gwamnan Tarayya ta amince da shi.

A ranar 5 ga watan Afrilu ne Darakta-Janar na hukumar, Birgediya Janar Olakunle Nafiu ya tabbatarwa ƴan hidimar ƙasar da suka kammala hidimarsu a lokacin cewa za a biya su da sabon tsarin biyan.

Da yake jawabi yayin taron wayar da kan ƴan zangon A na 2025, Birgediyan ya ce an ba su kuɗin domin biyan bashi wata biyu ga ɗaliban ciki har da waɗanda suka kammala a kwanan nan.

Ya kuma ce, gwamnati tana aiki tuƙuru wajen ganin ta amsa buƙatunsu ƴan Nijeriya a matakai daban-daban.

An biya su kuɗaɗen na hidimarsu daga watan Yulin 2024 zuwa Maris 2025 biyo bayan ƙorafe-ƙorafen jinkiri biyan nasu na tsawon watanni.

By Babaji