‘Yan sanda sun gayyaci El-Rufa’i da jagororin ADC kan zargin gwamnati da ba ƴan bindiga alawus

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda a Kaduna, ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa’i da wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC bisa zargin su da hannu a ƙulla makirci da ta da zaune-tsaye acikin al’umma.

A cewar rundunar ƴan sandan ta Mataimakin Kwamishinsu a jihar ɓangaren Cibiyar Bincike CID, Uzainu Abdullahi, an ba da takardar ne a ranar 4 ga Satumba, 2025.

A ciki an nemi El-Rufa’i da wasu mutane biyar da su je ofishin hukumar reshen CID a ranar 8 ga watan domin amsa tambayoyi nasu alaƙa da zarge-zargen da ake musu.

Sauran waɗanda aka gayyato tare da tsohon gwamnan sune: Bashir Sa’idu, Jafaru Sani, Ubaidullah Mohammed (aka 30), Nasiru Maikano, Aminu Abita da Ahmed Rufa’i Hussaini (aka Mikiya).

A halin yanzu sashen binciken yana gudanar da bincike akan mutanen da aka lissafo.

El-Rufa’i, wanda ya yi gwamna a jihar daga 2015 zuwa 2023, ya kasance ɗan siyasa mai wuyar al’amari duba da yadda ya ke sukar al’amuran siyasa a mataki na jiha da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji