2027: Tambuwal ya magantu kan rikici da Wike, ya yi mubayi’a ga Atiku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana aniyarsa ta mara wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar baya akan Ministan Abuja Nyesom Wike a zaɓen 2027.

Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels, Tambuwal ya ce biyayyarsa a siyasa cike take da sharuɗɗan jagoranci da goben Nijeriya ba ga wata alaƙar abota ba.

Tambuwal, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa a ya kan banbance alƙalar kai da hukunce-hukuncen siyasa don haka ake samun rashin jituwa tsakanin sa da jagororin siyasa a da da ƴanzu saboda salon tsarin nasa.

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan ya tunatar da lokacin da ya fice daga jam’iyyar PDP a zamanin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan, inda ya ce ya yi hakan ne saboda taɓarɓarewar harkokin jagorancin al’umma a lokacin.

Ya ƙara da cewa, duk da cewa akwai abota mai ƙarfi tsakaninsa da Wike, haka kuma akwai banbancin ra’ayi ta fuskar shugabanci.

By Babaji