Adadin ɓatan yara ya kai kashi 59 na ’yan Nijeriya 23,659 da suka ɓata

Spread the love

Daga MAHD MUSA MUHAMMAD

Aƙalla ’yan Nijeriya 23,659 suka ɓata da har yanzu ba a same su, lamarin da ya jefa iyalai 13,595 cikin ƙunci, kamar yadda rahoton kwamitin ƙasa da ƙasa na tallafi (ICRC) ya bayyana.

Jami’in ICRC, Benson Lee ya fitar da rahoton a Yola, kamar yadda rahotanni suka bayyana inda yayin jimamin ranar tunawa da mutanen da suka ɓata da tallafa wa iyalansu.

Lee ya bayyana cewa, yawan ɓatar mutane a Nijeriya na da alaƙa mai ƙarfi da yawan rikici tsakanin al’umma a matsanancin rashin tsaro a shiyyar Arewa-maso-Gabashin Nijeriya.

Ya ce, kaso 67 na al’amarin da suka samu rahoto a kai ya samo asali ne daga Jihar Borno sakamakon ayyukan ta da ƙayar baya na ƙungiyar Boko Haram.

Ya kuma yi ƙamari ne yayin suka gano cewa kaso 59 na mutanen yara ne marasa galihu, lamarin da ya nuna yadda rikici ke tasiri akan yara da marasa galihu.

Jami’in ya ƙara da cewa, wahalhalunda iyalan suke fuskanta a sanadiyyar tattali, shari’a da ma tsarin zamantakewa duba da cewa da dama daga cikin ɓatattun su ke ɗaukar nauyin iyalansu.

Da yake sanya halin da Nijeriya ke ciki a cikin tsarin duniya, Lee ya ce, “A cikin 2024, sama da mutane 94,000 ne iyalansu suka yi rajista a matsayin waɗanda suka ɓace ta hanyar ‘Family Links Network’, wanda ya kawo adadin waɗanda aka yi wa rajista zuwa kusan 284,400.

“Daga kwarewarmu wannan kaɗan ne kawai na adadin mutanen da suka ɓata.”

Wanda ya wakilci iyalan da abin ya shafa, Shugaban ƙungiyar Iyali na mutanen da suka ɓata, Luka Wada, ya bayyana godiya ga ICRC bisa ƙoƙarin da take yi na ganowa da kuma haca kan ‘yan uwa.

Ya koka da cewa kashi 80 na ɓacewar na da nasaba da tashe-tashen hankula, inda ya buƙaci ƙungiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati da su ba da tallafin kuɗi da na jinƙai ga ‘yan uwan ​​da aka bari a baya.

“Wasu daga cikin waɗanda suka bace ‘yan abinci ne, muna gode wa Allah da ya ba mu rayuwa, amma ba za mu iya mantawa da ‘yan uwanmu da suka ɓace ba,” inji Wada.

Ita ma a nata jawabin a wajen taron, shugaban hukumar samar da zaman lafiya ta jihar Adamawa, Dakta Jamila Suleiman, ta yi kira ga iyalan da abin ya shafa da su ci gaba da addu’a tare da fatan haɗuwa da ‘yan uwansu da suka ɓata.

“Hukumar tana aiki tuƙuru don inganta zaman lafiya a faɗin jihar domin hana tashe-tashen hankula da ka iya haifar da ɓacewar wasu mutane,” inji ta.

Suleiman ya tunatar da iyalai cewa ya kamata bala’in ɓacewar ya zama kira na ƙarfafa ƙoƙarin samar da zaman lafiya a cikin al’ummomin da ke fama da rikici.

Batun mutanen da suka ɓace ya zama ruwan dare gama gari a Nijeriya, musamman a jihohin da ake fama da tashe-tashen hankula kamar Borno, Adamawa, da Yobe, inda tashe-tashen hankula, ‘yan fashi da kuma rikicin ƙabilanci ke ci gaba da rura wutar ɓacewar mutane.

By ukarofi