DSS ta nemi X ta gaggauta rufe shafin Sowore kan sukar Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta buƙaci hukumar gudanarwar kafar X da ta gaggauta rufe shafin tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore.

A wata takardar koke da hukumar ta aike wa X, ta buƙaci a rufe shafin nasa a cikin sa’o’i 24.

Wani mai suna B. Bamigboye a madaɗin shugaban DSS, ya bayyana cewa matuƙar ba a rufe shafin ba, to za a ɗauki matakin doka a kai.

Ya ce, rubutun da Sowore ya yi game da Shugaba Bola Tinubu a ranar 25 ga watan Agusta kai iya haifar da hargitsi a ƙasar.

Ya yi ikirarin rubutun ɗan gwagwarmayarda ya wallafa abu ne na ruɗar da al’umma da cin mutunci, lamarin da a cewarsa zai iya haddasa fitina acikin magoya bayan shugaban ƙasar.

Haka kuma, ya ce hakan barazana ne ga tsaron ƙasa da mutunci Nijeriya a idon duniya, wanda saɓa wa sashe na 51 da dokokin manyan laifuka ƙarƙashin kundin dokokin yanar gizo na 2025 ne.

By Babaji