Birtaniya ta soke takunkumin shiga Jihar Kaduna akan ƴaƴanta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba Birtaniya ta sanar da janye taƙaice zirga-zirga ga ƴan ƙasarta bayan sanya musu takunkumin shiga Jihar Kaduna da ta yi a baya.

Daraktar Ofishin Ci-gaban harkokin Waje da na Arziƙin Ƙasa (FCDO), Cynthia Rowe ta bayyana haka yayin ƙulla yarjejeniyar tabbatar da bada tsaro ga ƴaƴan nata da gwamnatin jihar.

Ta bayyana cewa tun a shekarar 2022 aka sanya Kaduna a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da aka haramta wa ƴan ƙasar shiga sakamakon halin taɓarɓarewar harkokin tsaro a jihar.

Ta ce, an samu nasarar soke dokar ne sakamakon hoɓɓasa da Gwamna Uba Sani na jihar ya yi wajen warware matsalolin tsaro da suka dabaibaye sassan ƙananan hukumominsu.

Ana sa ran yarjejeniyar ta KaMAF, wadda gwamnan da Rowe suka sanya wa hannu, ta taimaka wajen samar da ci-gaba a shugabanci, lafiya, ilimi da noma.

Da yake jawabi, Gwamna Uba Sani ya bayyana nasarorin da aka samu ta haɗakar, inda ya ce sun haɗa da rage adadin mace-mace wajen haihuwa da yawan mutuwar ƙananan yara, sauƙaƙe hanyoyoyin kiwon lafiya, ingata makarantu da bai wa malamai horo.

By Babaji