Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Mataimakin Shugaban Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke ɓaɓura, Farfesa Ibrahim Sabo Birnin Kudu wato Federal University Of Technology Baɓura a Jihar Jigawa ya bayyana cewa samun masallacin Juma’a a wannan jami’a babban alkairi ne kuma babban burinsa da abinda yake so ya gani shi ne a samu ɗaliabai masu hazaƙa, tsoron Allah, ɗa,a da sanin ya kamata daga ɗaukacin al’ummar da ke wannan jami’a tun da kan ɗalibai, ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki na wannan jami’a ta FUT da ke ɓaɓura a Jihar Jigawa Nijeriya.
Farfesa Birnin Kudu ya bayyana haka ne a lokacin taron buɗe masallaci na farko a harabar jami’ar na wucin gadi a ranar Juma’ae da gabata.
Har ila yau mataimakin shugaban jami’ar FUT ya bayyana cewa wannan rana ce ta farin ciki da tarihi a wannan jami’a doimin babu abinda ya fi a ce Musulmi ya samu wurin ibadarsa wannan abun farin ciki ne kuma abun a godewa allah ne da wannan ni’ima inda kuma ya yi addu’a neman gafara ga Alhaji Abdu Shitu ɓaɓura bawan Allah da ya soma gina masallacin Allah ya karɓi rayuwarsa, da kuma fatan ƙaruwar arziƙi da ƙoshin lafiya ga Alhaji Aminu Ayuba bawan Allah da ya ƙarasa ginin masallacin.
A ƙarshe shugaban kwamitin ginin masallacin Malam Muntaƙa Idris Yunusa ya bayyan farkon wannan jami,a ma,aikata da ɗalibai na fuskantar matsalalolin ngurin yin sallah wannan ta sa suka fara tattara kwabo da ɗari domin samar da masallaci ko da na kamsus salawati ne a wannan to ana cikin haka sai Allah ya kawo wani bawan Allah yana aiki Allah da ikonsa ga shi yau anyi sallar farko a masallaci to wannan abun godiya da Allah kuma zamu kula da tsafta da raya masallacin da karatu kuma masallaci wani wuri ne na ibada da haɗa kan al’umma wuri ɗaya.
