Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon ƙaramin Ministan Harkokin Man Fetur, Ibe Kachikwu, ya bayyana cewa Marigayi Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi barazanar korarsa lokacin da ya bayar da shawarar a cire tallafin man fetur da kuma ƙara farashin litar man.
Kachikwu, wanda ya riƙe muƙami daga 2016 zuwa 2019, ya ce babban ƙalubalen da ya fuskanta lokacin da ya zama shugaban NNPC a 2015 shi ne dogayen layukan mai da suka durƙusar da tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce duk da ƙoƙarinsa, yawancin man tallafi ana fasa-ƙwaurinsa zuwa ƙasashen waje.
Ya bayyana cewa ya roƙi Buhari sau da dama a duba farashin mai, amma shugaban ya ƙi saboda matsayinsa na goyon bayan talakawa.
Daga bisani Buhari ya ce ya ɗauki haɗarin da kansa, idan ya yi tasiri shi kenan, idan bai yi ba kuma za a kore shi.
Kachikwu ya ce ya ɓullo da tsarin “price modulation” wanda ya dace da kasuwar duniya, inda hakan ya kawo ƙarshen tallafi kuma ya kawar da dogayen layukan mai cikin sa’o’i 48.
Ya kuma ce ya ki biyan tsoffin bashin tallafin da ya gada saboda ba shi da tabbacin gaskiya da ingancin da’awar.
