Ambaliya: Gwamnatin Katsina za ta siyo injinan tsane ruwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban hukumar kula da zaizayar Ƙasa da maganin ruwa ta Jihar Katsina (KEWMA), Alhaji Mannir Ayuba Sulluɓawa, ne ya bayyana hakan lokacin da ƙungiyar kansiloli ta jihar suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa.

Alhaji Sulluɓawa ya ce, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya amince da siyan injinan a matsayin wani mataki na gaggawa na kare al’umma daga barazanar ambaliya a birane da ƙauyuka a faɗin jihar.

Ya bayyana cewa akwai tabkuna da suke cike da ruwa, wanda hakan kan haddasa ambaliya da ka iya jawo asarar dukiya da rayuka.

” Saboda haka, hukumar ta KEWMA na ɗaukar matakai na kare muhalli da kyautata tsare-tsaren magance zaizayar ƙasa da ambaliyar ruwa,”inji Sulluɓawa.

Shugaban hukumar ya ƙara da cewa a kwanakin baya hukumar ta gudanar da taro tare da masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomi, domin wayar da kan al’umma kan haɗarin zaizayar ƙasa da ambaliyar ruwa da kuma hanyoyin kare kai.

Sai ya buƙaci kansiloli da su ƙara farfado da ƙungiyoyi na aikin gayya a yankunan su, domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnati da wajen kare muhalli.

Sulluɓawa ya jaddada cewa kofofin hukumar KEWMA a buɗe ta ke wajen haɗa kai da duk wanda ke da muradin bada gudummawa.

A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar kasilolin, Hon. Abdul Baki Tukur daga ƙaramar hukumar Ɓatagarawa, ya ce sun kawo ziyarar ne domin neman haɗin kai da goyon bayan hukumar KEWMA a fannin kula da muhalli a faɗin Jihar Katsina.

Hon Baki Tukur ya ƙara da cewa kungiyar nasu a shirye take ta bayar da dukkan goyon baya don ganin an cimma nasarar manufofin hukumar.

Ya yaba da yadda KEWMA ke gudanar da wayar da kan jama’a tare da godewa Gwamna Raɗɗa bisa ƙirƙira hukumar da nufin kare muhalli da rayukan al’umma.

By ukarofi