Kebbi: Majalisar Dokoki ta yi watsi da zargin ɗaukar nauyin tashin-tashina da Malami ya yi akan gwamnan jihar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dokoki a Kebbi ta yi tir da ƙorafin da tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya shigar akan Gwamna Nasir Idris, inda ya zarge shi da shigo da ƴan daba da sojojin haya daga waje domin haddasa tarzoma a jihar.

Da yake ganawa da manema labarai a farfajiyar majalisar, Kakakinta, Hon. Muhammad Usman ya bayyana zargin Malamin a matsayin zance mara asali da aka kiekida nufin ruɗar da al’umma.

Hon. Usman ya ce, jihar Kebbi waje ne da ke da daraja da kima a idon al’umma a matsayinta na ɗaya daga cikin jihohi masu tsaro don hana duk wani yunƙuri na zubar da kimar, hari ne kai-tsaye akan al’ummarta.

Ya kuma ce, hakan ba ya rasa nasaba da ƙoƙarin karkatar da hankalin gwamnatin jihar daga ayyukan ci-gaba da take shimfiɗa wa al’umma zuwa wani abin da ka iya haifar da cikas.

Ya ƙara da cewa, babu wata hujja da ke alaƙanta gwamnatin jihar da abinda yake zargin ta a kai na hayar ƴan dabar siyasa, safarar makamai ko haɗa hannu da sojojin haya.

A cewar kakakin, baki ɗaya hukumomin tsaro da ke aiki a jihar sun tabbatar da cewa babu wani rahoton sirri da ke goyon bayan abinda Malami ke ikirari a kai.

By Babaji