
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu miyagu a babura sun daɓa wa wani bajamuse wuƙa tare da yi masa fashi a Birnin Tarayya Abuja.
A cewar SaharaReporters, wani rahoton tsaro ya bayyana cewa al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na safiyar Asabar akan titin IBB way, kusa da makarantar firamare ta Maitama.
Ɗan Jamus din, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya haɗu da iftila’in ne a lokacin da ya ke tafiya a gefen hanya a ƙafa, inda wasu ƴan daba a babura suka cimmasa.
An gano cewa, sun caka masa wuƙa sannan suka jefar da shi a gefen titi kana suka tsere da wasu ababensa.
Rahoton ya kuma bayyana yadda al’amarin tsaro ya ke neman caɓewa a birnin musamman wajen amfani da babura yayin fashi akan ƴan ƙasa da waɗanda ba su ba.
Haka kuma, ya gargaɗi al’umma da su ƙara kulawa game yanayin zirga-zirgarsu a birnin, yana mai kira a gare su da su ƙaurace wa tafiyar kaɗai, bayyana ababe masu daraja da kiyaye amfani da ababen sufuri da aka amince da su.
