Ribas: An fara shirye-shiryen koma wa mulkin dimukraɗiyya a jihar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Ribas ta fara gudanar da shirye-shiryen koma wa mulkin dimukraɗiyya daga na dokar ta-ɓaci a jihar.

Sakataren gwamnatin, Farfesa Ibibia Lucky Worika ya sanar da haka a wata takarda.

A cewarsa, an gayyaci baki ɗaya masu ruwa da tsaki zuwa interdenominatuonal church thanksgiving service a yau Lahadi.

Waɗanda aka gayyata sune manyan sakatarori, ciyamomin ƙananan hukumomi, jagororin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, jagororin hukumomi da sauransu.

Kantoman jihar, Ibok-Ete Ibas shi ne baƙo na musamman a taron.

By Babaji