Likitoci sun janye yajin aiki

Spread the love

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara a ranar Juma’a sakamakon ƙorafe-ƙorafen da suka shafi rashin kulawa da lamuran ƴaƴanta daga ɓangaren gwamnati.

A wata sanarwa da NARD ta fitar, ta ce ta janye yajin aikin na kwana biyar ne bayan Gwamnatin Tarayya ta amince da fara biyan wasu daga cikin buƙatunsu.

“Bayan yunƙurin da gwamnati ta nuna na biyan wasu buƙatun da muka sanar, da kuma shirin fara biyan alawus ga ma’aikatan da ke bin bashi…mun amince mu janye yajin aikin daga ƙarfe 8:00 na safiyar Lahadi,” inji sanarwar.

Ta ƙara da cewa, ta bai wa gwamnatin tarayyar wa’adin mako biyu domin aiwatar da alƙawuran da ta ɗauka.

By Babaji