Ƙungiyar haɗin kan Funtua ta samar wa mutanen yankin guraben aiki

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman ya sanar da haka a wata takardar sanarwa da ya fitar.

kwamred Suleiman wanda shine a samar da guraben aikin ya bayyana cewa masu sha’awar aiki a jami’o’i da su tuntuɓi sakatariyar ƙungiyar zuwa garin Bakori “su kuma je da takardar karatun su,”inji shugaban.

Ya ce wannan ƙoƙari na ɗaya daga cikin yunƙurin da ƙungiyar take yi wajen samar da aikin yi a yankin.

“Guraben aikin sun haɗa da sashin magunguna,ɗakin gwaje-gwaje da sauran gurabe akan abinda ya shafi harkar lafiya,”kwamred Suleiman ya ce.

Kwamred Suleiman ya jaddada ƙudirin ƙungiyar na ƙara zaƙulo guraben aiki a ma’aikatu da hukumomi na gwamnatin tarayya domin amfanin al’ummar yankin da jihar Katsina baki ɗaya.

Ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa bai wa yan asalin yankin Funtua manyan muƙamai daban daban a gwamnatin sa.

By ukarofi