Ambaliya: Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jihohi 14

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta yi aiken sabon saƙon gargaɗi da al’ummomin garuruwa 52 a jihohi 14 da ke sassan Nijeriya.

Ta yi haka ne domin ankarar da su game da yiwuwar aukuwar ambaliya a tsakanin ranakun 16 da 18 na Satumba, 2025, inda ta kiraye su da shirya wa al’amarin.

Cibiyar Gargaɗin Ambaliya akan Lokaci ta Ƙasa (NFEWC) ƙarƙashin Ma’aikatar Kula da Muhalli a wani rahoto da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan kula da lamuran ambaliya da yankunan ruwa Usman Abdullahi Bokani, ta bada gargaɗin tare da kira ga gwamnatocin jihohi, hukumomi da yankuna masu barazanar ambaliya da su faɗaɗa kulawa da ɗaukar matakan da suka dace.

Rahoton ya lissafo jihohin da kuma yankunan nasu kamar haka:
Akwa-Ibom: Upenekang, Eket, Edor, Oron, Ikot Abasi, Ikot-Ekpene, Etinan, Uyo, Obianga

Anambra: Ogbakuba, Nnewi
Adamawa: Yola, Wuro Bokki, Farkumo, Jimeta Kuros-Riba: Akpap, Calabar
Bayelsa: Amasoma, Ikpidiama, Kalama, Yenagoa, Peremabiri, Sagbama, Oporoma, Odoni, Otuoke, Kolokuma/Opokuma, Ogbia, Oliobiri. Delta: Patani, Asaba, Abari, Escravos, Umuochi Utchi
Kaduna: Kachia, Kauru Kebbi: Birnin Kebbi, Kalgo Katsina: Bakori Ribas: Ahoada, Bonny, Itu, Bori Imo: Egbema, Oguta Sakkwato: Argungu, Gagawu, Silame Ondo: Igbokoda, Ore, Okitipupa Legas: Epe

Haka na zuwa ne kwanaki uku da aka yi irin gargaɗin ga jihohi Adamawa da wasu 10 musamman al’umma a yankunan da ke da kusanci da kogunan Gongola, Benuwai da Neja.

By Babaji