Tinubu ya dawo Nijeriya bayan kammala hutu a Turai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A jiya Talata Shugaba Bola Tinubu ya koma Abuja bayan kammala hutunsa na shekara a Nahiyar Turai.

Da fari ya sauka ne a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja inda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa suka marabce shi.

Haka kuma, daga ciki akwai Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila da Ministan Tattali Wale Edun.

Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da dawowar Shugaban Ƙasar a wata sanarwa ta ranar Litinin inda ya ce shugaban ya kammala hutun nasa, sannan ana sa ran ya koma bakin aiki a ranar Talata.

Tun a 4 ga watan Satumba, 2025 Tinubu ya bar Nijeriya zuwa Faransa da nufin raba hutun nasa a ƙasar da kuma Ingila.

A yayin zamansa na Faris, Tinubu ya yi ganawar sirri da Shugaba Emmanuel Macron na ƙasar a Fadar ‘Élysée Palace’.

Shugabannin sun tattauna muhimman batutuwa da suka haɗu a kai da kuma cin alwashin ƙarfafa alaƙa don ci-gaba da ɗorewar harkokin tattali a mataki na duniya.

By Babaji