
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa game da halin da ƴan Nijeriya ke ciki na tsananin yunwa da talauci, yana mai gargaɗi cewa hakan na iya janyo rikice-rikicen zamantakewa a ƙasar.
A sanarwa da ya fitar ranar Litinin, ya ce rayuwar yawancin ƴan ƙasa ta taɓarɓare kuma hakan na haifar da matsanancin rashin jin daɗi ga al’umma, wanda ke iya barazana ga zaman lafiya da ɗorewar dimukraɗiyya a ƙasar.
Atiki Abubakar ya kuma ce rashin tsari mai kyau a harkokin tattalin arziƙi da rashin kulawa daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya na daga cikin abubuwan da ke haifar da matsin lambar ga al’umma.
Kazalika, Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa don rage radadin matsin rayuwa da samar da hanyoyin tallafawa al’umma.
Ya tuna yadda yunwa da talauci suka haddasa juyin juya halin Faransa, juyin juya halin Rasha na 1917, da kuma “Farkawar Larabawa” wanda ya fara daga Tunisia ya bazu zuwa gabas ta tsakiya da Arewacin Afirka.
Atiku ya gargadi gwamnati da cewa halin da ake ciki yanzu na iya zama wata hanya ta tunani da gyara, don kauce wa irin waɗannan tashin hankali da tarihi ya nuna.
