
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya tabbatar wa al’ummar jiharsa cewa gwamnatinsa za ta cigaba da aiki tuƙuru tare da la’akari da muradunsu da ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnati da al’umma.
Gwamnan ya faɗi haka ne a yau Juma’a yayin da ya isa gidan gwamnatin jihar tun bayan dakatarwar da Shugaba Bola Tinubu ya masa watanni shida da suka gabata, inda ya samu gagarumar tarba daga jama’a.
Ya ce, karɓarsa da al’ummar suka yi ta nuna yadda soyayya da haɗin kai ke da ƙarfi acikin su, inda ya jinjina musu a bisa hakan tare da nuna farin cikinsa a gare su.
A cewarsa, hakan abu ne da ke ƙara tabbatar da yadda suka yi amanna da gwamnatinsa da tsare-tsarenta.
Haka kuma a yi alƙawarin cewa gwamnatin nasa za ta cigaba da samar da tsare-tsare da za su dace da buƙatun al’ummar jihar.
A watan Maris Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar bayan rikicin siyasa ya yi ƙamari tsakanin zaɓaɓɓun ƴan siyasa.
