Yobe: Shugaban ƙaramar Hukumar Bade ya yaba wa Gwamna Buni kan cigaba

Spread the love

Daga GAMBO ISA a Abuja

Shugaban ƙaramar Hukumar Bade a Jihar Yobe, Hon. Ibrahim Babagana, ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni na jihar ta Yobe bisa manyan nasarorin da ya samu a fannin bunƙasa ɗan Adam, samar da ababen more rayuwa, noma, ilimi, da kiwon lafiya a faɗin jihar.

A wata sanarwa da Babagana ya raba wa jaridar Blueprint a Abuja, ya yi ƙarin haske game da gyaran babbar sakatariyar ƙaramar hukumar Bade, samar da fitilun titi mai amfani da hasken rana, gina cibiyar gudanar da taro, da hanyoyi a matsayin wasu muhimman ayyukan da gwamnan ya yi waɗanda suka shafi ƙaramar hukumar kai tsaye.

A fannin kiwon lafiya kuwa, ya lura da gina wuraren shan magani 21, da cibiyoyin kiwon lafiya nmatakin farko guda biyu, da ɗaukar ma’aikatan lafiya 57. Ya ƙara da cewa gwamnati ta kuma samar da babura masu uku don sauƙaƙa jigilar ma’aikatan lafiya tare da tallafawa ayyukan kula da koda domin inganta harkokin kiwon lafiya a Bade da kewaye.

Har ila yau ilimi a cewar shugaban ya samu ci gaba tare da gyare-gyaren wasu makarantun firamare da sakandare da suka haɗa da ƙarin ɗakunan karatu, ɗakunan ma’aikata, da banɗakuna. Ya yaba wa gwamnan bisa aiwatar da sabon mafi karancin albashi ga malamai da kuma tallafawa shirye-shiryen horar da likitoci, ma’aikatan jinya, da ungozoma domin ɗaukaka harkar lafiya da ilimi.

A fannin noma, Babagana ya yaba da samar da taraktoci, taki, da sauran kayan aiki a ƙarƙashin kashi na ɗaya da na biyu na shirin noma na jiha, tare da samar da wuraren kiwo kyauta domin bunƙasa dangantakar manoma da makiyaya cikin lumana. Ya kuma bukaci matasa da su rungumi sana’o’in hannu, koyon sana’o’i, da dogaro da kai, inda ya ce gwamnan ya kuma dauki ma’aikata 50 da suka kammala karatu aiki a unguwanni goma na Bade.

Shugaban ya bayyana Gwamna Buni a matsayin shugaba mai hangen nesa wanda manufofinsa suka kawo sauyi ga rayuwa tare da samun karɓuwa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa. Ya yi alƙawarin biyayya ga ƙaramar hukumar Bade ga aikin gwamnan tare da yin kira ga shugabannin al’umma, matasa, da mazauna yankin da su tallafa wa shirye-shiryen gwamnati tare da ci gaba da addu’ar zaman lafiya da ci gaban jihar Yobe da Nijeriya.

By ukarofi