Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Ministan Tsare-tsaren Kasafi da Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya roƙi Hukumar Haɗin Gwiwar Jirgin Sama ta ƙasa da ƙasa ta Japan (JICA) da ta ƙara ƙoƙari wajen jawo hankalin ‘yan kasuwa masu zuba jari daga Japan zuwa Nijeriya.
Bagudu ya yi wannan magana ne a lokacin da sabon wakilin JICA a Nijeriya, Mista Ishigame Keiji, ya kai masa ziyarar ban girma. Keiji ya maye gurbin Mista Yuzurio Susumu, wanda ya shafe shekaru uku da watanni shida yana aiki a matsayin Wakilin JICA a Nijeriya.
Muna son masu zuba jari su shigo Nijeriya domin mu na da sha’awar samun goyon bayanku wajen bunƙasa harkokin masu zaman kansu.
Mun daidaita tattalin arziƙin ƙasa, kuma muna da tubalin da zai iya tallafawa ayyukan masu zaman kansu da za su ƙara haɓaka kasuwanci da samar da kaya.
Sabon wakilin JICA, Keiji, ya bayyana cewa Nijeriya ƙasa ce mai matuƙar muhimmanci, mai tattalin arziƙi mai kuzari da dama na ci gaba. Ya kuma shaida wa ministan cewa ana shirin faɗaɗa ayyuka a Nijeriya da Japan, domin gwamnatin Japan tana da niyyar tallafawa Nijeriya wajen cimma Manufofin Cigaban ɗorewa (SDGs).
Wakilin hukumar mai barin gado Mista Susumu, ya bayyana farin cikin yin aiki tare da gwamnatin Nijeriya, inda ya yi alkawarin ci gaba da tallata da faɗaɗa ayyukan da ake gudanarwa a Nijeriya yayin da ya koma hedikwatar JICA Tokyo a ƙasarsa ta Japan.
Tun da farko, Mukaddashin Babban Sakataren Ma’aikatar, Dr. Sampson Ebimaro, ya bayyana cewa akwai dogon tarihin alaƙa tsakanin JICA/Japan da Nijeriya. Ya kuma yaba da goyon bayan Japan a fannonin ilimi, lafiya, gine-ginen more rayuwa, samar da wutar lantarki, da tabbatar da zaman lafiya.
JICA ta kasance tana tallafa wa shirye-shirye a Nijeriya da nufin inganta rayuwar al’umma da bunƙasa tattalin arziƙi. ɗaya daga cikin sabbin shirye-shiryenta shi ne haɗin gwiwa wajen kafa cibiyar ƙirƙira (innovation hub) da kuma aikin wutar lantarki na dala miliyan $238 domin inganta kayayyakin more rayuwa da shirye-shiryen horarwa. A baya kuma, JICA ta tallafa a fannin ilimin firamare, lafiya (musamman wajen yaki da cutar zazzabin cizon sauro), da kuma ci gaban aikin gona.
