Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bayanan Babban Bankin Nijeriya (CBN) sun nuna cewa Naira ta lallasa dalar Amurka zuwa N1,497.46 kan kowane dala, saɓanin N1,501.49 da aka yi cinikinta a baya.
Wannan na nufin cewa Naira ta ƙara daraja da kashi 0.27, karon farko da kuɗin Nijeriyar ya tumurmusa dalar Amurka a kasuwar canji a cikin watanni bakwai.
A watan Fabrairun 2025 ne aka yi cinikin Naira a aasa da N1,500 a kasuwar musayar kuɗi ta hukuma, amma tun lokacin, dalar Amurka ke tashi sama.
Wannan farfaɗowar da Naira ta yi ta zo ne bayan mako guda da darajarta ta ke zuwa N1,500, amma tana gaza sauka zuwa ƙasa.
An kuma samu irin wannan ci gaban a kasuwar bayan fage, inda aka riƙa cinikin Naira da Dala kan N1,535, kamar yadda rahoton CardinalStone Research ya nuna.
Rahotannin kasuwa sun nuna cewa Naira ta kasance tana ƙara daraja da 0.98% a kowanne mako, inda ta koma N1,501.50 kan dala a kasuwar gwamnati, da N1,535 a kasuwar bayan fage.
A cewar rahoton mako-mako na Coronation, darajar canjin kuɗi a hukumance ta aaru da N35.50 ko kashi 2.23, mafi girma da na kasuwar bayan fage.
Rahoton ya kuma nuna cewa jimillar musayar kuɗaɗen waje da suka shigo Nijeriya sun kai dala miliyan 550.90 a makon da ya gabata, wanda ya dan yi ƙasa da dala miliyan 567.20 da aka samu a makonni biyu da suka gabata.
Zuba hannun jari daga ‘yan kasuwar ƙasashen waje (FPI) ne suka mamaye kuɗaɗen da suka shigo ƙasar, wanda ya kai dala miliyan 303.8 ko kuma 55.15.
Sauran hanyoyin da aka samu walwalar dalar sun haɗa da ɓangaren masu fitar da kayayyaki zuwa waje (17.61), da kamfanoni da ba na banki ba (17.57).
Sauran kamfanoni sun bayar da 4.32, sannan masu zuba jari na kai tsaye su ba da 3.39, CBN ya ba da 2.36, sannan kuma ɗaiɗaikun mutane sun ba da 0.60.
An ce tsare-tsaren CBN sun taimaka wajen daidaitar farashin Naira a kasuwar hada-hadar kuɗi.
Masana sun ce karuwar darajar Naira ya samo asali ne daga yawan shigowar kudaden zuba jari daga kasashen waje, da karuwar ajiyar kuɗaɗen waje, da kuma tasirin tsare-tsaren CBN.
Masana a kamfanin AIICO Capital sun ce wadatar dalar Amurka daga FPIs, masu fitar da fetur, da kuma kuɗin shiga daga aasashen waje sun ƙara daraja Naira.
Ana ganin Naira, a kasuwar hada-hadar kuɗi za ta ci gaba da samun ƙarfi saboda manufofin CBN da ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da wadatar dala.
Har ila yau, rahotanni sun nuna cewa ajiyar kuɗin waje na Nijeriya ya karu zuwa dala biliyan 41.69, abin da zai ci gaba da ƙarfafa kasuwar da kuma tabbatar da daidaito ga Naira.
