Buga tiriliyan 22.7 a gwamnatin Buhari ya sa Naira faɗuwa – Dogara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya zargi gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari da lalata tattalin arzikin Nijeriya.

Dogara, wanda yanzu shi ne shugaban NCGC, ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin wani taro da Majalisar Wakilai ta shirya.

Ya ce matakan tattalin arzikin da aka ɗauka a lokacin gwamnatin Buhari sun jefa ƙasar cikin mawuyacin hali, musamman ta hanyar buga kuɗi.

Dogara ya bayyana cewa sama da Naira Tiriliyan 22.7 aka buga aka zuba cikin tattalin arziki a lokacin Muhammadu Buhari.

Ya ƙara da cewa, tsarin musayar kuɗi da aka yi a baya ya ba wasu mutane damar samun riba mai yawa ba tare da samar da wani kaya ko sabis ba.

A cewarsa, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki, tattalin arzikin Nijeriya ya riga ya zama “gurɓatacce” kuma yana buƙatar sauyi da gaggawa.

Dogara ya ce, daga ranar farko, shugabancin Tinubu ya ɗauki matakai na gyaran tattalin arziki domin kauce wa rugujewar ƙasa.

Ya bayyana waɗannan matakai a matsayin masu muhimmanci ga ci gaban Nijeriya, wanda zai shafi ilimi, kiwon lafiya, tsaro da kuma gine-gine.

Dogara ya bayyana kafa kwamitin Shugaban Kasa kan manufofin haraji da Dr Taiwo Oyedele ke jagoranta a matsayin muhimmin mataki na sauya tsarin ƙasa.

Ya ce, kwamitin ya fito da shawarwarin sauye-sauye masu tasiri da za su canza dokoki da ƙa’idojin da suka tsufa domin samar da adalci da daidaito.

Sai dai ya jaddada cewa duk wani gyara na tattalin arziki yana fuskantar ƙalubale daga waɗanda suke cin gajiyar tsohon tsarin.

Dogara ya ce, an fuskanci adawa mai tsanani daga ɓangarorin da ke amfana da tsofaffin dokoki da tsarin tattalin arziki.

A cewarsa, nasarar sauye-sauyen da ake son cimmawa na buƙatar dabaru, jajircewa da kuma hadin kan masu ruwa da tsaki domin cimma burin ƙasa.

By ukarofi