Dan adawar zanga-zangar EndSars, Buhun Barkono, ya mutu a otel a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yunusa Ahmadu Yusuf, wanda aka fi sani da Buhun Barkono, shahararren mai sukar zanga-zangar EndSARS a watan Oktoban 2020, ya mutu a wani otel tare da mace a Abuja.

Kungiyar EndSARS, wacce ta ɗauki tsawon kwanaki 14 a shekarar 2020 a faɗin manyan biranen Nijeriya tana zanga-zanga, ta buƙaci a rusa rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta musamman da ke yaƙi da ‘yan fashi da makami, da ta shahara wajen zalunci da kashe-kashe da kuma cin hanci da rashawa.

Zanga-zangar wacce da farko ta fara yaƙi a shafukan sada zumunta, ta fantsama, inda ta ɗauki wani mummunan yanayi a ranar 20 ga watan Oktoba, 2020, lokacin da aka zargi jami’an tsaron Nijeriya da buɗe wuta kan masu zanga-zangar da ba su ɗauke da makamai a ƙofar Lekki Toll, lamarin da ya janyo cece-ku-ce a duniya da kuma ƙin amincewa da gwamnatin lokacin.

Yusuf, wanda ya yi aiki a matsayin babban mataimaki na musamman kan ci gaban al’umma ga shugaban ƙaramar hukumar Abuja Municipal Area Council (AMAC), Christopher Zakka Maikalangu, ya rasu kwanaki bayan ya kwanta a otel a ranar Talata, 8 ga Satumba, 2025, a unguwar Karu-Jikwoyi a babban birnin tarayya.

A cewar SaharaReporters, Yusuf mai shekaru 47, ya shiga cikin otel ɗin tare da wata mata mai suna Ruth. A lokacin zamansa, ya ƙi abinci amma ya sha barasa da yawa.

Da safiyar mutuwarsa, Ruth ta saya masa wani abin sha bayan ta lura da yanayinsa. Jim kaɗan da ɗaukar ta ne Yusuf ya faɗa cikin duguwar suma.

Ma’aikatan otel da Ruth sun garzaya da shi wani asibiti da ke kusa, amma ya mutu da isar sa.

Tuni dai ‘yan sanda suka fara gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin halin da ya faru da mutuwarsa.

Yusuf a matsayin babban mai adawa da zanga-zangar EndSARS:

Yusuf, wanda aka fi sani da Buhun Barkono (AMAC), an san shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu adawa da zanga-zangar #EndSARS ta nuna rashin amincewa da zaluncin ‘yan sanda a babban birnin tarayya.

A watan Oktoban 2020, Yunusa Ahmadu Yusuf, a cikin wata wasika da ya aike wa Sufeto Janar na ‘yan sanda na lokacin, Mohammed Adamu, ya buƙaci masu zanga-zangar #EndSARS da su bar manyan tituna a babban birnin tarayya Abuja. Ya ce zanga-zangar na kawo cikas ga harkokin tattalin arziki da zamantakewa a Abuja.

Da yake magana a madadin ‘yan asalin babban birnin tarayya Abuja, Yusuf ya bayyana takaicin su, inda ya yi gargaɗin cewa sunadaf da yin fushi.

A yayin da take nuna ɓacin rai kan mace-macen da aka samu a lokacin zanga-zangar, ƙungiyar ta kuma koka kan yadda toshe hanyoyin ke haifarwa da illoli, inda ta yi nuni da cewa amfanin gonakin noma na rubewa, kuma masu samun albashi na yau da kullum na fama da yunwa saboda kwastomomi ba za su iya shiga kasuwa ba.

A wani saƙon da ya wallafa a Facebook a ranar 22 ga Oktoba, 2020, Yusuf ya yi iƙirarin cewa wasu ɓata gari sun shiga zanga-zangar.

Yusuf ya kuma bai wa masu zanga-zangar wa’adin sa’o’i 48 su bar hanyoyin babban birnin ƙasar.

By ukarofi