Kwamitin aikin hajjin 2025 na Jihar Filato ya miƙa rahotonsa ga Gwamna Mutfwang

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Kwamitin da aka ɗora wa alhakin shiryawa da gudanar da hidimar aikin hajjin bana da ya gabata, ƙarƙashin hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta Jihar Filato, ya miƙa wa Gwamnan jihar Caleb Manasseh Mutfwang rahoton sa.

Da yake miƙa rahoton, Amirul Hajj na bana, Mai Martaba Sarkin Wase, Dr Muhammadu Sambo Haruna na ll ya bayyana jin daɗinsa da yadda aka samu nasarori masu yawa a wannan shekarar fiye da a shekarun baya. Sannan ya yaba da irin haɗin kan da sauran ýan kwamitin da hukumar Alhazai ta jiha suka ba shi, wanda ya taimaka wajen samun nasarorin da aka yi.

Ya kuma sanar da gwamnan irin halayen ƙwarai da alhazan Jihar Filato suka nuna a yayin zaman su a ƙasa mai tsarki, wanda hakan ya sa suka samu yabo sosai daga hukumomi da sauran jama’a. Daga ciki akwai wata ýar jihar da ta tsinci wasu maƙudan kuɗaɗe har Dalar Amurka dubu 500, wanda tuni aka miƙa su ga mai su. Harwayau, akwai wani Alhaji da shi ma ya tsinci wata babbar waya ƙirar iPhone kuma ýa mayar da ita.

Gwamna Caleb Mutfwang wanda ya bayyana jin daɗinsa da waɗannan nasarori da aka samu ya yi alƙawarin sakantawa waɗannan alhazai da suka nuna halayen ƙwarai, tare da ƙara jan hankalin sauran al’ummar Filato baki ɗaya da su zama jakadun ƙwarai ga Jihar Filato a duk inda suka samu kansu.

Ya kuma jinjinawa Amirul Hajj da sauran ýan kwamitin kula da jigilar aikin Hajjin bisa sadaukarwa da riƙon amanar da suka nuna. Ya ƙara da kiran shugabannin al’ummar musulmi na jihar su cigaba da nuna kyakkyawan jagoranci ga mabiyansu don samun ɗorewar zaman lafiya da cigaban Filato baki ɗaya.

By ukarofi