An kama shi a Kano kwanaki da yi wa babban mawaƙi fashi a Legas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano, ta ce ta yi nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannun a laifin fashi da yunƙurin kisa ga wani sanannen mawaƙi a Nijeriya, wato Lil Kesh da wani mazaunin Legas.

Kakakin ƴan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da haka a wata takarda, inda ya ce hakan ya samu ne a ranar 11 ga watan Satumba sakamakon aikin bin diddigi da jami’ai suka yi bayan samun wasu bayanan sirri.

Waɗanda aka kaman sune Matthew Adewale mai shekaru 25 da wani Mukhtar Muhammad ɗan shekara 31 a yankin Unguwa Uku da ke jihar Kano.

A cewar rahoton binciken ƴan sanda, mutane biyun suna da alaƙa da harin da aka kai a rukunin gidaje na Bera da ke Chevron Drive a Legas, inda a nan Lil Kesh yake da zama.

A yayin al’amarin, wanda ya faru a ranar 19 ga watan Agusta, 2025 aka samu mawaƙin, inda a nan aka masa dukan da ya kai ga ya galabaita.

Da fari, rundunar ƴan sandan Legas ta fara bincike akan lamarin, wanda ya ta da hazo a kafafen sada zumunta kana daga bisani binciken sirri ya fallasa maɓoyarsu a Kano.

Bayan kamen ne aka miƙa su ga rundunar ta Legas domin cigaba da bincike akansu da kuma yiwuwar gurfanar da su a kotu.

By Babaji