
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) karo na 80 da za a yi a birnin New York da ke Amurka.
Za a gudanar da shi ne daga ranar Litinin, 22 zuwa Lahadi, 28 ga Satumba, 2025.
A sanarwar da Kakakinsa Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce za a yi haka ne bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu.
Shettima zai gabatar da jawabi a madadin Nijeriya ranar Laraba, 24 ga Satumba a tsakanin ƙarfe 3 na rana zuwa 9 na dare agogon New York.
Haka kuma zai halarci taro na musamman kan lamuran yanayi da za a yi tsakanin shugabannin ƙasashe, wanda Sakatare Janar na MƊD zai jagoranta, inda mataimakin shugaban ƙasar zai gabatar da gudumawar ƙasa na NDCs a ƙarƙashin yarjejeniyar Paris.
Sauran ayyukan da wakilin Nijeriyar zai yi sun haɗa da zaman ƙasashen da suka yi fice wajen samar da wadatattun gine-gine masu rahusa da Shugaban Kenya zai jagoranta.
Baya ga haka ne zai tafi Frankfurt a ƙasar Jamus inda zai gana da manyan jami’an bankin ƙasar, wato Deutsche Bank.
