
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da bincike akan wata sabuwar cutar fata da ta ɓulla, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane bakwai bayan da dama sun kamu da ita a wani ƙauyen Jihar Adamawa.
Kodinetan riƙo na shirin kula da cutukan tarin fuka, fata da sanyi mai tsanani, Dakta Adesigbin Olufemi ya tabbatar da al’amarin a wata hira da manema labarai, ranar Lahadi.
A cewarsa, zuwa 10 ga watanni Satumba an samu tabbacin mutane 68 sun kamu da cutar, inda takwas daga ciki nasu ya yi tsanani waɗanda a yanzu suke Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama da ke Yola.
Cutar, wadda ta jefa al’ummar Malabu cikin fargaba, ta fara ne daga manyan ƙuraje da ke fashewa idan sun girma daga bisani kuma suke lalata fata da ƙasusuwa yayin da suka yi ƙamari.
A yayin bincike ne aka gano cewa cutar ta ɓulla ne sakamakon samun cutar fata ta ‘Buruli Ulcer’, wadda ake yawan samun ta a yankunan ruwa.
