Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Ƙungiyar masana harkar guba ta Najeriya (Toxinological Society of Nigeria TSN) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da na jihohi da su mai da hankali wajen zuba jari a samar da maganin cizon maciji a cikin gida tare da inganta cibiyoyin kiwon lafiya, domin daƙile mace-macen da ke faruwa sakamakon cizon maciji a ƙasar.
Wannan kira ya fito ne daga sanarwar bayan taro da babban sakatare na TSN, Dokta Mustapha Shehu Muhammad, ya fitar bayan taron nasu karo na biyu na ƙungiyar, wanda aka gudanar daga 14 zuwa 17 ga watan Satumba a Jami’ar Gombe.
Taron ya tattaro fiye da mahalarta 1,000, ciki har da likitoci, masana bincike, shugabannin gargajiya, ɗalibai da kuma masu tsara manufofi.
Taken taron shi ne: “Bincike kan Samar da Maganin Cizon Maciji a Cikin Gida da Jinya a Najeriya: Manufofi, ƙalubale da damar da ke ciki.”
Masana sun bayyana cewa Najeriya na fuskantar aƙalla cizon maciji dubu 43,000 a duk shekara, wanda ke haddasa mutuwar fiye da mutane 1,900. Sun ce yara na daga cikin mafiya fuskantar barazanar, inda su kaɗai ke kai kashi 30 cikin dari na waɗanda ake cizon.
An nuna cewa jinkirin samun magani, tsadarsa da kuma rashin isassun cibiyoyin kiwon lafiya, na daga cikin manyan matsalolin da ke janyo mace-mace, musamman a yankunan karkara.
A jawabi da Farfesa Abdulrazak Habib, ya gabatar a lokacin ya jaddada buƙatar gwamnati da masu zaman kansu su yi gaggawar saka hannun jari a samar da maganin cikin gida, domin rage mace-mace da kuma asarar tattalin arziki.
Baya ga taron, mahalarta sun kai ziyara Asibitin Kula da cizon maciji na Kaltungo, inda suka shaida yadda yake cike da marasa lafiya fiye da kima. Sun yi kira da a faɗaɗa asibitin tare da samar da ƙarin kayan aiki.
A cikin shawarwarin da ƙungiyar ta bayar sun haɗa da:
Kafa cibiyar ƙasa ta ƙwararru kan Maciji, maganin cizon Maciji da guba a Gombe.
Ɗaga darajar asibitin Kaltungo zuwa matsayin asibitin ƙasa na cizon Maciji tare da kayan aiki na zamani da tsarin sa ido.
Ta buƙaci gwamnatin jihar Gombe ta ware aƙalla kashi ɗaya na kuɗaɗen shigarta na cikin gida domin yaƙi da cizon maciji, ciki har da samar da magani kyauta.
Haɗa darussa da bincike kan cizon maciji a manhajar Jami’ar Gombe.
