2027: Ƙungiyar APC a Zamfara ta amince da Matawalle a matsayin ɗan takarar gwamna

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gamayyar ƙungiyar siyasa ƙarƙashin jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara da aka fi sani da Talban Anka Coalition ta amince da ƙaramin ministan tsaro Hon. Bello Mohammed Matawalle ya zama ɗan takarar gwamna a zaɓen 2027 a jihar.

Shugaban ƙungiyar kuma tsohon kwamishinan filaye da gidaje Hon. Sharu Dan Sarki ya bayyana haka a yayin wani taro da aka gudanar a babban masaukin baki da ke Gusau “Command Guest Inn” yau Asabar.

Ya bayyana cewa ƙungiyar a shirye take ta marawa Matawalle baya domin ya zama Gwamnan Zamfara na gaba a zaɓen 2027.

Dan Sarki ya ci gaba da cewa ƙungiyarsa za ta ci gaba da zama a APC maimakon haifar da ɓaraka a tsakanin mambobin ta a jihar.

A cewarsa, an haɗe kungiyoyin siyasa 20 daga mazaɓar Zamfara ta yamma a ƙarkashin shugabanci sa, mai suna Talban Anka Coalition, domin marawa Matawalle don tsayawa takarar gwamna a 2027.

A cewar sa, ƙungiyar ta ga ya dace ta bar tafiya jam’iyyar APC ɓangaren Hon. Aminu Sani Jaji Domin su jaddada goyon bayan su ga tafiyar Sanata Abdulaziz Yari da ƙaramin ministan tsaro Hon. Bello Mohammed Matawalle domin cigaban jam’iyyar a jihar.

Da yake karɓar ƙungiyar, shugaban jam’iyyar APC na jihar Hon. Tukur Danfulani wanda ya samu wakilcin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Yusuf Idris ya ba su tabbacin cewa za a tafi dasu bai ɗaya ba tare da nuna banbanci ba.

Ya kuma buƙaci ‘ya’yan jam’iyyar APC da magoya bayan jam’iyyar a jihar, da su ci gaba da kasancewa tare domin ci gaban jam’iyyar.

By ukarofi