Matatar Ɗangote ta koma sayar da fetur da Naira

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Matatar man fetur ta Ɗangote ta sanar da koma wa sayar da fetur da kuɗin Naira ga kwastomominta.

Hakan na zuwa ne a lokacin da kwamitin gudanarwa na sayar da mai da Naira ya shiga tsakani bayan matakin farko da ta ɗauka na janyewa daga cigaba da amfani da kuɗin wajen cinikayyar fetur tsakaninta da su.

Kamfanin ya faɗi haka ne a wata takarda da ya aika wa kwastomomin nasa a yammacin jiya Asabar, 27 ga Satumba, 2025, inda ya ce matakin zai fara aiki ne a nan take.

Don haka ta kiraye su da su cigaba da zuwa saye a farashin Naira daga ko’ina a faɗin ƙasar.

Da fari, kamfanin a ranar Juma’a, 26 ga watan nan na Satumba ya sanar da dakatar da sayarwa da Naira, inda ya bada hujja da ƙarewar wa’adin cinikinsa da kuɗin na Nijeriya bisa yarjejeniyar da suka ƙulla da masu ruwa da tsaki.

By Babaji