
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ƙoƙarinta na yaƙi da miyagun laifuka, rundunar ƴan sanda a Abuja ta yi nasarar kama sanannun ƴan ‘one chance’ guda bakwai da suka addabi al’umma a babbar birnin, waɗanda ake zargin su da hannu a kisan ƴar hidimar ƙasa (NYSC).
Haka kuma ta ce, jami’anta sun ƙwato wata mota da aka sace bayan ɗauki ba daɗi tsakaninsu da ƴan fashi a birnin tarayyar.
A wata takarda daga hukumar, majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’an bayan samun bayanan sirri, sun kama waɗanda ake zargi da hannu a kisan Mis Oluchi Opara Glory, wadda ta kammala hidimarta a Abuja kwanan nan.
A ranar 25 ga watan Satumba, 2025 aka gudanar da kamen bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga lauyoyin Onyegbula Akujuobi & Co. Practitioners zuwa ga Sufeto-Janar na rundunar.
Akan haka rundunar, reshen Abuja, ta ƙaddamar da atisayen a ƙarƙashin tawagar Scorpion Squad.
Waɗanda kaman sune: Solomon Obada (29), Olemba Ajonwe (29), Aba Godwin (40), Kadijat Yakubu (18), Sunday Ejih Okpeh (29), Joseph Oche Samuel (25), da Michael Sunday Eneh (25).
Rundunar ta ƙara da cewa, har yanzu akwai waɗanda cigaba da farauta akan al’amarin.
A wani ɓangare, jami’an hukumar sun yi nasarar daƙile wani shirin ƴan fashi na kai hari a rukunin gidaje NNPC da ke unguwar Karmo a yankin Life Camp da misalin ƙarfe 3:45 da daren Alhamis wayewar Juma’a.
