PTD ta nemi Tinubu ya tsoma baki a takun sakar PENGASSAN sa Matatar Ɗangote

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tawagar direbobin tankokin fetur (PTD) reshen NUPENG ya kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta shiga tsakani yayin da ta zargi jagorancin Ƙungiyar manyan ma’aikatan fetur da gas ta ƙasa (PENGASSAN) da ƙoƙarin wuce iyakarta wajen ƙoƙarin daƙile nasarorin da matatar mai ta ɗangote ta samu.

PTD ta kuma tabbatar wa sauran masu ruwa da tsaki cewa babu wani abin ɗaga hankali game da barazanar PENGASSAN ta shiga yajin aiki.

Kwamared Obi-Dede Wonder a madadin jagororin PTD ya bayyana haka a wata takarda a Abuja.

Ya ce, babu wani batu na sallamar ma’aikata guda 800 daga matatar Ɗangote aka maye gurbinsu da sama da Indiyawa 2,000 ba su da sahihan takardun shiga Nijeriya, labarin da a cewarsa abu ne da aka ƙirƙira da ba shi da asali.

Ya bayyana hakan a matsayin gazawa daga wata ƙungiyar da yunƙurin tada zaune-tsaye a harkokin fetur tsakaninta da matatar.

Kazalika, ya yabi hukumar gudanarwar Matatar Ɗangote bisa yadda ta ke kula da ma’aikatanta da ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci wajen kiyaye ƴancinsu a matsayin ƴan ƙasa kuma waɗanda ke aiki a ƙarƙashinta.

By Babaji