
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Kamfanonin Raba Wutar Lantarki, Ruwa, Gas davaay (PURC) ta ce akwai yiwuwar kuɗin lantarki da al’umma ke biya ya ƙaru da kashi 1.14 daga yanzu zuwa ranar 1 ga watan Oktoba, 2025.
A cewar hukumar, sauyin zai samu ne sakamakon nazari akan farashi na zangon ɗaya bisa huɗu na shekarar da ake ciki.
Hakan zai samu ne sakamakon sauyin kuɗaɗen waje ciki har da na sidin Ghana da Dalar Amurka da sauran ababen da suka shafin fannin.
A sanarwar da Sakataren riƙo na hukumar, Shafic Suleman ya fitar, ya ce hakan ya zama wajibi domin bai wa kamfanonin lantarki da na ruwa damar cigaba da samarwa al’umma cikin walwala.
