
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta musanta ikirarin da wasu kafafen watsa labarai na ƙasa-da-ƙasa da masu sharhi ta yanar gizo ke yi na zargin ƴan ta’adda a Nijeriya suna yi wa ƴan addinin Kirista kisan kiyashi.
A wata takarda da jaridar NewsPointNigeria ta samo a ranar Lahadi, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya bayyana zarge-zargen a matsayin zantukan ƙarya da ake yaɗawa da ke ƙoƙarin raba kan al’ummar Nijeriya da haddasa gaba a tsakaninsu.
Ya ce, ba daidai ba ne a riƙa yi wa lamarin ƙalubalen tsaro a ƙasar mummunan fahimta da za a danganta shi da addinin, inda ya tirje akan hakan abu ne da ya shafi rayuka da dukiyoyin kowane addini da ƙabila a ƙasar.
Minista Idris ya bayyana cewa, sanannen abu ne cewa hare-haren ƴan ta’adda abu ne na ‘kan mai uwa-da-wabi’ da ya shafi Musulumi, Kirista da ma waɗanda ba su da addini, wanda a cewarsa, rashin adalci ne a ce ɓangare ɗaya iftila’in ya shafa.
Ya cigaba da cewa, a tsakanin wata Mayu, 2023 da Fabarairun 2025, jami’an tsaro sun yi nasarar halaka ƴan ta’adda da masu manyan laifuka guda 13,543 tare da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su kusan su 10,000.
Haka kuma, ya yi tuni da babbar nasarar da jami’an tsaro suka yi yayin wani atisaye a watan da ya gabata na kama jagororin ƙungiyar ‘Jama’atu Ansarul Muslimina fi-Biladis Sudan’ da aka sani da ANSARU, wadda ke wakiltar Al-Ƙaida a Nijeriya.
Kazalika, ya ce Nijeriya ta yi nasara a yaƙi da Boko Haram inda aka gurfanar da masu hannu a ciki a kotu, wanda zuwa yanzu an samu aƙalla mutum 700 da hannu a laifin a shari’a guda bakwai da aka yi akan waɗanda ake zargi.
A ƙarshe, ya yi kira ga gidajen jaridu musamman a mataki na ƙasa-da-ƙasa da masu sharhi da su riƙa ƙaurace wa ƙarairayi da ake yaɗawa da ka iya haddasa tarzoma acikin al’umma da kuma tsaiko ga nasarorin da ake samu a yaƙi da ta’addanci a Nijeriya.
