
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta yi magiya ga ƙungiyar manyan ma’aikatan fetur da gas PENGASSAN, da ta dakatar da yajin aikin da ta shirya kan rikicinta da Matatar Ɗangote.
Ministan Ƙwadago da Ɗaukar aiki, Muhammad Dingyaɗi ya bayyana haka a wata takarda a Abuja, ranar Lahadi.
Ƙasa da sa’o’i 48 da suka gabata ne PENGASSAN ta umarci mambobinta da su janye daga cigaba da gudanar da ayyukansu akan zargin sallamar ma’aikata ƴan Nijeriya a daga aiki a Matatar ta Ɗangote.
Ƙungiyar ta PENGASSAN ta zargi hukumar gudanarwar Ɗangote da ayyukan tsangwama da nuna wariya akan ma’aikata ƴan gida, lamarin da ya sa gwamnatin tarayyar ta tsoma baki domin shawo kan matsalar.
Minista Dingyaɗi ya ce, tuni ma’aikatarsu ta fara aikin sulhunta tsakanin ɓangarorin biyu domin kauce wa ƙamarin rikicin.
Ya kuma roƙi dukkansu da su kula da muhimmancin al’amarin fannin fetur, wanda shi ne ƙashin bayan tattalin arziƙin ƙasa.
A yau Litinin za a gudanar da zama tsakanin wakilan ɓangarorin biyu a ofishin ministan da ke Abuja.
