Ruftawar wajen haƙar ma’adinan Zamfara: Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da atisayen ceto

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da atisayen ceto a yankin Kadauri da ke Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara, inda wani sashe na wajen haƙar ma’adanai ya rufta tare da halaka masu aiki da dama.

Ministan Ci-gaban Albarkatun Ƙasa, Dakta Dele Alake a wata takarda ta mai taimaka masa akan harkar yaɗa labarai, Segun Tomori ya bayyana haka a jiya Lahadi.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito cewa lamarin ya auku ne a daren ranar Alhamis wayewar Juma’a, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 10, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.

An danganta al’amarin da yawaitar masu kutse cikin aikin ba bisa doka ba da sauran haramtattun ayyuka.

Ministan ya ce, suna aiki tare da haɗin-gwiwar jami’an gwamnatin jihar wajen ceto mutanen da iftila’in ya afka wa, wanda da zarar an kammala, za a rufe wajen.

Ya ƙara da cewa, jami’an haƙar ma’adanai na jihar za su jagoranci atisayen ceto, bincike game da musabbabin faruwarsa da kuma gabatar da gamsasshen rahoto a kai.

A cewarsa, mutane suna rige-rige yayin da suka ji labarin an gano wani waje da ke da gwala-gwalai tare da yin watsi da gargaɗi akan sha’anin muhalli da haɗarin da hakan ka iya haifar wa rayukansu.

Ya bayyana cewa, akan haka ne gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke ƙoƙarin daƙile ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba ta amfani da atisayen sojoji da ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA) ya shirya.

By Babaji