Ƙungiyar ahlussunnah ta yi tir da kalaman Mataimakin Gwamnan Kano cewa an siyasantar da batun Abduljabbar da Lawan Triumph

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Haɗakar malaman Ahlussunnah Wal-Jama’ah ta Kano ta yi tir da kalaman Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo cewa hukuncin da aka yanke wa Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara kan ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) abu ne da aka siyasantar da shi.

A wata takarda da ta fitar ta hannun Farfesa Muhammad Muslim Ibrahim, tawagar malaman ta ce furucin nasa abu ne da zai iya jefa al’umma cikin ruɗani duba da cewa kotu ta riga ta yanke masa hukunci.

A jiya Lahadi, 28 ga watan nan na Satumba, 2025, Mataimakin gwamnan ya yi tsokaci akan lamarin a lokacin da yake jawabi a taron Maulidi da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Malam Bazullahi Sheikh Nasiru Kabara a Masallacin Juma’a na Turasul Islam da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a jihar.

Tawagar malaman ta ce, hakan da mataimakin gwamnan ya yi zai iya sa al’umma su fara zargin ko akwai wata rufa-rufa acikin al’amarin wajen yunƙurin sako Abduljabbar ko kuma ƙoƙarin cune wa wasu malamai kamar Sheikh Lawan Abubakar Shu’aibu Triumph da irin zargin.

Ta bayyana cewa, Abduljabbar a fili ya yi kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta, lamarin da ya sa aka tutsiye shi domin ya kare kansa. Ganin hakan bai samu ba ya sa shari’a ta yi aiki akansa da yanke masa hukuncin da ya dace da shi bisa adalci.

Don haka, ta yi alla-wadai da dukkan wani yunƙuri na siyasantar da lamarin da ya shafi taɓa daraja da kimar Manzon Allah (SAW).

Kazalika, ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta fitar da matsayarta a fili akan al’amarin Abduljabbar ga al’umma, waɗanda haƙƙinsu ne akanta ta sanar da su.

A ƙarshe, Ahlussunnah Wal-Jama’ah ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a jihar da su cigaba da aiki tuƙuru wajen kare martabar addini, girmama shari’a da tabbatar da kare darajar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).

By Babaji