Kotu ta umarci Sufeto Janar ya kama Shugaban INEC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Osogbo, babban birnin jihar Osun, ta umarci Sufeto Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun da ya kama Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu bisa nuna raini ga kotu da ƙin biyayya ga dokokin ƙasa.

Mai shari’a, Funmilola Demi-Ajayi ta bayyana haka a ranar Litinin bayan jam’iyyar AA (Action Alliance) ta shigar da ƙara akan INEC.

Alƙalin ta ce, da Farfesa Yakubu da hukumar zaɓen sun yi buris da hukuncin da aka yi da fari na tabbatar da shugabannin jam’iyyar na jihohi ƙarƙashin jagorancin Adekunle Rufai Omoaje daga majalisar zartarwar (NEC) jam’iyyar.

Jam’iyyar AA ta lauyanta K.O. Etibo ta nemi kotun da ta tasa ƙeyar Shugaban na INEC zuwa gida yari kan abinda ta kira da yin ƙememe wajen bijire wa umarnin kotu.

A yayin hukuncin, kotun ta bayyana cewa rashin bin umarnin ya nuna cewa Farfesan ya raina matsayin kotun da dokokin ƙasa don haka ta amince da buƙatar hakan.

Bugu da ƙari, Alƙalin ta sanya tarar N100,000 akan Shugaban na INEC.

Daga nan sai ta umarci INEC da Yakubu da su dawo da sunayen baki ɗaya shugabannin jam’iyyar na jihohi, ƙarƙashin jagorancin Omoaje zuwa shafinta acikin mako guda ko kuma su fuskanci tilas daga hukumar ƴan sanda.

By Babaji