Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kiyaye Haɗura ta ƙasa FRSC ta bayyana yadda wasu direbobi masu tuƙin ganganci a watan Satumba 2025 suka kashe jami’an hukumar biyar yayin da suke kan aikinsu.
Bisa ga takardar da jami’in wayar da kan jama’a na Hukumar Olusegun Ogungbemide ya fitar ranar Talata ya nuna cewa hakan ya faru ne a sassa biyar na Hukumar da ke faɗin ƙasar nan a tsakanin wata ɗaya.
Ya ce sassa da ranakun da jami’an hukumar suka gamu da ajalin sun haɗa fa ranar 6 ga Satumba a Ekiti, ranar 8 ga Satumba a sannan Ogun, ranar 15 a sannan Taraba, ranar 19 a garin Jos jihar Filato da ranar 24 a Obollo.
Shugaban Hukumar FRSC, Shehu Mohammed, wanda ya bayyana mutuwar a matsayin “abin bakin ciki matuƙa,” ya ba da umarnin a gurfanar da duk direbobin da ke da hannu a kotu domin ya zama tirjiya.
Hukumar FRSCl ta nuna damuwarta kan yadda samar wa jami’an hukumar kariya ke ci gaba da taɓarɓarewar inda ya ce ga gudun ababen hawa, jami’an na ƙara fuskantar munanan hare-hare, garkuwa da mutane da sauransu.
Ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ta sake lamuntar ayyukan da ke barazana ga ma’aikatanta ba, yana mai jaddada cewa masu laifin za su fuskanci mummunan sakamako na shari’a.
