
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya amince da aikin titin kilomita 100 na Legas zuwa Kalaba, wanda zai rastsa ta yankin Jihar Edo.
Ministan Ayyuka, Dave Umahi ya sanar da haka a yayin sanya ido akan wani ɓangaren aikin tagwayen titin Benin zuwa Warri na Edo da ba a ƙarasa ba, ranar Alhamis.
Da yake tsokaci akan halin rashin kyawun hanyar, Ministan ya ce babu wani mai abin hawa da zai yi tuƙi har na tsawon kilomita 100 a titunan gwamnatin tarayya ba tare da fuskantar ƙalubalen lalacewar wasu wurare ba, yana mai cewa hakan abu ne da shugaban ƙasar ya gada daga ayyukan da gwamnatocin baya suka bayar.
Ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu kan yadda ya nuna damuwa game da al’amarin da amincewa da cigaba da ayyukan don amfani al’umma da ma ƙasa baki ɗaya inda ya jinjina wa masu-ruwa-da-tsaki ciki har da Shugaban gidan talabijin na Arise, Nduka Obaighena.
Umahi ya ƙara da cewa amince wa aikin da Tinubu ya yi sakamako ne na biyayya, shugabanci da ƙoƙarin sauke nauyin jagorancin.
Da yake jawabi, Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya yi godiya ga mai girma Shugaba Tinubu bisa abinda ya kira da inganta ayyukan ababen more rayuwa a jihar.
