
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Alhamis, Elon Musk ya zama mutum na farko a duniya da ya mallaki arziƙin da jimillarsa ya kai kimanin Dala biliyan 500.
A cewar U.S. magazine Forbes, hakan ya samu ne sakamakon kasancewarsa attajirin da ke da hannun jari a kamfanonin electric carmaker Tesla da aerospace firm SpaceX.
Mujallar ta lissafo dukiyar Musk, wanda aƙalla ta kai Dala biliyan 150, wanda hakan ke nuna ya fi wanda ya samar da kamfanin Oracle, wato Larry Ellison.
Daga bisani ta sake ƙididdige arziƙin har zuwa Dala biliyan 499.1.
Arziƙin attajirin ba kamar na sauran attajirai ba, na da wahalar lissafawa duba da cewa wasu kamfanoninsa ba bayyane ake tallata su ba.
