Tsohon sanata ya shiga hannun ƴan sanda kan zargin fyaɗe ga ƴar shekara 13

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon sanatan da ke wakiltar Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo ya miƙa kansa ga Hukumar ƴan sanda ɓangaren binciken manyan laifuka (FCID) a Abuja bayan an zarge shi da yi wa ɗalibar makarantar sakandare mai shekaru 13 fyaɗe.

Blueprint ta ruwaito cewa ana kan aiki akan batun duk da cewa wasu sanannun ƴan Adamawa sun yi ƙoƙarin sanyaya gwiwar iyayen yarinyar don su janye daga ƙorafi a kai.

Wakilin jaridar ya ruwaito cewa iyayen sum shaida wa ƴan jarida cewa tsohon sanatan kuma ɗan takarar gwamna, ya sha ziyarar gidan su yarinyar domin roƙon su kada su bayyana al’amarin.

Sun kuma yi zargin cewa bayan faruwar al’amarin a ranar 29 ga watan Yuni, 2025 a gidan Abbo da ke Katampe a Abuja, tsohon sanatan ya sha aika wa mahaifin yarinyar kuɗi domin rufe masa baki akan lamarin.

Yunƙurin jin matakin binciken ta bakin Kakakin ƴan sandan, CSP Benjamin Hundeyin ya ci tura kasancewar ba a same shi a waya ba sannan bai amsa saƙon da aka aika masa ba.

An taɓa kama Sanata Abbo a shekarar 2019 bayan wani faifan bidiyo ya nuna yadda ya ci zarafin wata mata a wani shagon sayar da kayan saduwa da kai a Abuja.

Haka ma wata matar aure ta taɓa zargin sa da yi mata sharri da wani bidiyon batsa.

By Babaji