Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Legas ta kama wani mai-gadi mai suna Amos Kini, bisa zargin sace wani yaro ɗan shekara biyu a unguwar Elemoro.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abimbola Adebisi, ta fitar a yau Litinin, ta bayyana cewa mahaifiyar yaron ce ta kai rahoton lamarin makon da ya gabata.
Sanarwar ta ce, “Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 11:50 na dare, lokacin da mahaifiyar yaron ta kai rahoto a sashen ‘yansanda na Elemoro cewa ma’aikacin tsaronta ya gudu da ɗanta da wayarta ba tare da izini ba.”
Bayan haka, wanda ake zargi ya yi amfani da wayar da ya sace wajen kiran mahaifin yaron, inda ya nemi kuɗin fansa na Naira miliyan biyar (N5,000,000) kafin ya sake shi.
Kakakin rundunar ta ce jami’an tsaro sun kuma kama wani mutum mai suna Aruna Dauda, wanda ya tsaya wa wanda ake zargi shaida kafin a ɗauke shi aiki, domin gudanar da tambayoyi.
Daga baya wanda ake zargin ya saki yaron, amma rundunar ta ci gaba da farautarsa domin tabbatar da an kai shi ga hukunci.
“A ranar 23 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 2:00 na rana, jami’an sashin Tactical Sƙuad (Hyena), bayan samun sahihan bayanai, sun gano inda yake, suka kuma cafke Amos Kini a cikin unguwar Elemoro. Wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma yana hannun ‘yan sanda. Za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike,” in ji Adebisi.
