
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Asabar Shugaba Bola Tinubu zai je Jos, Babban Birnin Jihar Filato domin ziyarar aiki ta kwana ɗaya da kuma miƙa ta’aziyyarsa tare da gaisuwa ga jagororin addini a Arewa.
A wata sanarwa da Kakakinsa Bayo Onanuga ya fitar a jiya Juma’a, Shugaban ƙasar zai halarci taron addu’ar rasuwar marigayiya Nana Lydia Yiltwatda Goshwe, wato mahaifiya ga Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nantewe Yiltwatda Goshwe.
Tinubu zai haɗu da iyalai da abokan siyasa da abokan arziƙi domin karrama marigayiyar, wadda ta rasu yayin da take tsaka da yi wa al’umma hidima bisa sadaukarwa.
Baya ga haka Shugaban ƙasar zai yi ganawar sirri da jagororin addinin Kirista a hedikwatar cocinsu na COCIN, wanda ɗaya ne daga cikin manya kuma daɗaɗɗun ɗariku a shiyyar.
Hakan wani ɓangare ne da ke nuna yadda Tinubu ke ƙoƙarin samar da haɗin kai da jituwa tsakanin addinai a Nijeriya musamman duba da halin matsin tsaro da ƙalubalen rayuwar yau da kullum acikin al’umma.
A ranar ne kuma ake tsammanin Shugaban ƙasar ya wuce jihar Legas bayan kammala ayyukansa na Jos domin wasu muhimman ayyuka.
